🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*YAKI DA RASHIN GASKIYYA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Tare da
*Maryam S Indabawa (Antty)*
*MANS*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S*
*HAJOW*
*```(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)```
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
~Dan Allah ku bada minti kadan dan ku karu da abinda ke ciki. In fa ka zamo mai alfahari da addinin ka da kuma son tarbiyar ya'yan ka da kanenen ka da yayun ka~
```Ina godiya da Allah da ya bani ikon zama marubuciyya domin marubuci na kwarai aikin sa isar da sako ga al'umma. Sakon kuma mai mahimmanci wanda yake fadakar wa, wato ya ilimantar da al'umma ta yadda zasu fa'idan tu su san aibun abun tare da sakamakon mai aikata abun. Sai kuma nishadantar wa da muke. To Alhamdulilah yau mun shigo da fadakarwa aakan wani abu da yake neman ya zama gama gari kowa na yin sa. Wanda wannan abu ba karamin aiki ne na sabawa ga Allah Madaukakin sarki.```
Nasan zaku so kuji ko akan me nake ta wannan maganar. Akwai abubuwa da yawa da muke sabawa Allah (SWT) amman zan dauko wannan maudu'in saboda abun ya kazan ta. Kazanta ba kadan ba ma.
Nasan kun zuba Ido kuga akan me zanyi magana ko? To ba akan komai bane sai akan *Madigo* wanda daga mata har maza ke yin sa. Wato mata suna yin *(Lesbian)* maza kuma suna yin *(Homo)*
*Inna lillahi wainna illaihir rajiun!*
*Inna lillahi wainna illaihir rajiun!!*
*Inna lillahi wainna illaihir rajiun!!!*
Hakika wannan mumunar d'abi'a ce wacce aikata ta mummunar jaraba ce ga rayuwar wanda ke yi da al'umma baki daya.
Dan wannan d'abi'ar ba karamar shafar rayuwar mu take ba. Ko ta cikin irin wadan nan masifun da Allah ke jarabar kasashen mu duk dan mun kaucewa Allah ne.
Hakikanin gaskiya wannan kazanta ce mata. Allah ya haramta. kada ku manta akan wannan d'abi'ar sai da aka dulmiyar da al'umma guda amman hakan bai tsorata mu da munisance ta ba.
Hakika d'abi'ar madigo tafi ta zina haka nan tana daya daga cikin manyan Laifufuka wanda in har muka dawama da aikata su hakikanin gaskiya bazamu taba samun rahamar ubangiji ba.
Wannan d'abi'a da muka dauka da farko kazanta ce tayaya ma zaka nemi dan uwan jinsin ka. Dan haka Allah ya hallarta mana aure dan mu raya sunna mu kuma samu nutsuwa daga mazan mu da matayen mu.
Tayaya muke zaton zamu samu haka daga yan uwan jinsin mu. Hakika muna aikata babban zunubi wanda in har bamu tuba ba muna cikin bala'i da masifa.
Haba yar uwa kiyi aure mana ko dan samun ladan sunnah da raya sunna ba ki zauna ki/ka na mu'alama da yar uwar ki/ka ba wacce duk abinda ke ajikin ki yake a jikin ta dame zaki amfana kenan. Wanda duk abinda zaku aikata hakika kina aikata abinda kullun kina cikin kuncin rayuwa da masifar rayuwa. Haba yar uwa ki kiman ta kanki, ki rufawa kanki asiri kiyi aure ki samu dadi da ladan aure wanda duk abinda kikai a gidan auren ki lada zaki samu. Ba abinda zaki nayi mala'iku na tsine miki ba.
Ko kin manta irin cuttukan da ake samu ta hanyar yin lesbian.
*Shin kinsan illar da kikewa kan ki kuwa?*
Wallahi cututtukan da ake kamuwa da su ba kananun cuta bane.
*Da farko Allah na fushi dake da kike aikata babban zunubi wanda in har baki tuba ba Allah zai hukunta ki dan wannan babbar masifa ce. Dan bake ba rahamar Allah. Wanda kowa abinda yake nema kenan a rayuwar sa.
*Na biyu zaki rasa mutuncin ki dan zaki rasa budurcin ki. In ma ya tsaya anan kenan.
*Na uku Zaki kamu da ciwo kala kala wasu daga nan kansa ke shigar su ai ta fama neman magani har a rasa daga baya ki zauna gu daya dan duk kin cinye farjin ki sai wari da tsotsotsi da zasuyi tayi.
Akwai illoli masu yawa wanda duk kaji su sai hankalin ku ya tashi dan wannan ba karamar matsala bace.
Haba ya kai Dan uwa akan me zaka nemi dan uwan dan ka biya bukatar ka da shi.
Wa'iyazubillah!
Inna lillahi wainna illahir rajiun!
Yan uwa kuji fa. Wai mutum ya nemi 'Dan uwan sa wannan wace irin masifa da bala'i ne. Haba ya kai dan uwa na, shin me zaka nema a gun dan uwan ka wanda in har kai aure ba zaka same shi gun matar ka ba.
Wallahi ahunda zaka sama gun matar ka ya fi maka wannan sau malala gashin tinkiya.
Wanda in kayi Auren nan zaka samu nustuwa, kwanciyyar hankali, lada, ni'ima karin lafiya. Amman kai ka ki ko? Ka tafi wajen da Mala'ikun Allah ke tsine maka kana kara kwasar wa kan ka masifa da bala'i.
*```Illar madigo (Homo)```*
*Rashin samun Rahamar Daga gun Allah.*
*Fuskantar tashin hankali saboda yadda Allah ke fushi da kai*
*Kullum cikin damuwa da kuncin rayuwa.*
*Illata jiki, yadda zaka iya rasa haihuwa ma.*
*Kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki*
*Lalacewar al aura*
```Haba yan uwa in kun lura da illar wadan nan abubuwan da zasu faru da kai ka yi yaya da rayuwar ka.```
Amman a haka wannan d'abi'ar ke ci ke ta habbaka tare da yin gaba a rayuwar nan wacce ba abinda ya fita yin gaba a rayuwa yanzu.
Wai akan wannan harkar har waje ake fitar da mata haka har kasa mai tsarki suke zuwa dan aikata wannan mummunar d'abi'ar.
Wa'iyazubillah! Shin me kike nema, *Dukiya* ko me?
Hakika kunyi kuskure in har dan haka kuke yi dan in dan samun nutsuea ne to baku taba samun nutsuwa in har ba aure kukai ba.
Wai har aure ake yi jinsi da jinsi. Ina zamu kai wannan aikin asha, shin ta haka Allah madaukakin sarki yace mu yi aure mu auri jinsin mu?
In dan kudi ne ki sani wallahi kudin nan bazai tabai miki albarka ba.
Haba ya ke yar uwa ki rasa me zaki sabawa Allah sai sabawa akan raya sunna ke ki canja ki ce yar uwar jinsin ki zaki aura
*Yake yar uwa me kike nema da har kika kai kan ki ga halaka.*
*Yake yar uwa kinsa lokacin da zaki mutu*
*Yake yar uwa me kike samu ga wannan banzar D'adibar*
*Yake yar uwa kiyi karatun ta nutsu ki gane me kike aikatawa da illar sa.*
Wai har bin malamai da bokaye ake dan a kara jan mutum ta karfi da yaji ake. Zunubi goma da ashirin kenan ga na madigo ga na bin malamai shin ina zamu kai wannan mummunar aikin da muke yi.
To shawara anan da zan bamu gaba dayan mu shine mu dage da addu'a Allah ya kare mu daga duk sharrin mutum da Aljanna. Dan wannan babban bala'i ne ke tin karar mu.
Kar kuji ina ta magana akan wannan mummunar d'abi'ar kuce ko ita kadai ce abinda aka haramta.
A'ah amman tana daya daga cikin manyan zunuban da bama fatan Allah ya jarabace mu da su.
*Ina son dan jan hankali ga iyaye tare da mazaje da yayun mu maza da mata akan lura da d'abi'un yaran su*
*Ya ku iyayen mu ina mai son jan hankalin ku akan illar da hakan ke jawo wa gare mu dan duk abinda ya'yan mu suka yi har damu yake shafa. Dan har mu yake jawo wa.*
*Iyaye yana da kyau muna sa ido akan Halaiyar yaran mu.*
*Da farko irin kawayen da suke kulawa. Yana da kyau muna kula da irin kawayen da ya'yan su ke kulawa, dan kawa na taka babbar gudunmawa akan lalata tarbiyar ya'yan ku. Dan haka muna kula da irin kawayen da ya'yan mu suke shiga akai.*
*Na biyu irin d'abi'un da suke, yana da kyau muna kula da yadda yaran mu ke gudanar da wasu d'abi'un su na rayuwa ta yadda suke shigar su da mu'amala da mutane.*
*Na uku Akan me muka sakar wa ya'yan mu rayuwar su har muka basu manyan wayoyi wanda irin wadan nan wayoyin na matukar bada gudunmawa wajen bata tarbiyar yaran mu dan yana da kyau muna bincika su ba mun basu abu mu zuba musu ido kawai ba.*
```Yana da kyau muna dubawa ba a kan idon su ba dan muga irin groups din da suke ciki da irin kawayen da suke mu'amala da su da irin chat din da suke.```
```Tabbas muka saka ido akan ya'yan mu tare da musu addu'a to zamu ci riba a rayuwa tare da samun yara nutsatsu.```
Mu dage da addu'a akan yaran mu da nema musu shiriya.
*Mu lura da masu wadan nan d'abi'un*
Duk masu yin lesbian zaka same su masu son nuna tsuraicin su,
*da son taba jikin mace, ko yabar jikin ta. Da bada sunayen da bai kamata ba wanda in ba soyayya ake ko mata da Miji ba baza ka ji su ba*
*da son yin ado a part din da ba kowa ke gani ba kamar cibiya da kasan harshe,*
*haka nan zaka same su masu saka zobe ko sarkar kafa, zaka ga yawancin su da bular hanci, haka nan suna saka zobe a babban dan yatsan su na hannu*
Ya ku masu irin wadan nan d'abi'un ina kira daku akan kuji tsoran Allah ku daina, kusani zaku mutu kuma za kuje ku tarar da dukkan abinda kuka aikata, mai kyau ko akasin haka.
Gwara ku aikata mai kyau dan ku sani lahira gaskiya ce kuma wuta ma haka duk abinda ka aikata zaka je ka girbe shi
*wallahi in bamu daina wannan 'dabi'ar ba, ba abinda zai hana mu shiga wuta dan Allah ya fadi karshen masu wadan nan abubuwan*
*_Anan nake addu'a ga Allah da ya shirye duk mai wannan d'abi'un. Mu kuma Allah ka shirya mu ka kare mu, muda zuri'ar mu baki daya. Allah ka tsare mana imanin mu a duk inda muke. Ameen Ya hayyu ya Qaiyum_*
*Ya Allah ka shirya mu.*
*Ya Allah ka shirya zuri'ar mu*
*Ya Allah ka shirya mmuslmai baki daya*
*Ameen Ya Rab*
Taku har kullum
*Msindabawa*
(Antty)
WhatsApp
08034860550
No comments:
Post a Comment