Tuesday, December 25, 2018

LAIFINA NE part 1-5

*🍡🍡🍡🙆🏽‍♀LAIFI NANE 🙆🏽‍♀🍡🍡🍡*

*STORY...............*

*WRITTEN BY MRS SADEEQ ✍🏻*
*(Ummu meenal)*

*True lyf story*

*🌟GORGEOUS WRITER'S FORUM🌟*

                   *G.R.F*

*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we the best among the rest*

*DEDICATED TO MARYAM AMINU JUMARE (majmiy)*

*Note*
*Tabbas labarin dayake cikin wannan littafin gaskiya ne ma'ana abun ya faru da gaske, kwanannna wacce abun ya faru a kanta ta ro'keni da in rubuta labarin ta hakan zaiyi tasiri a zuciyar 'Yan mata da da samari*
*bayan haka wacce abun ya faru akan ta tabbas nasan ta duk da cewa ta umurceni da in 6oye sunan ta,*
*saboda haka zanyi amfani da wani suna na daban can Amma labarin dayake ciki tabba ya faru da gaske😭*

*page 1-5*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Fatima! Fatima!! Fatima!!!,
Wata matashiyar budurwa ta fito daga cikin wani ďaki tazo wajen inda ake kiranta,

Wani ďaki tashiga da alama anan ne ake ' kwala mata kira,
Kai tsaye naga ta tsaya dai dai wajen wata mata da alama itace mahaifiyar ta,

Matar wacce zatakai kimamin shekaru arba'in tace" haba Fatima kina ina nake ta kiranki haka? ",

Fatima tace" wallahi mama ina ďaki banji kiran da kike yimun ba sai yanzu ",

Maman Fatima tace" kedai Fatima baki gajiya da kwanciya kullum kina ďaki ko gajiya da kwanciya bakiyi, kinga ga amina nan batada lafiya tun jiya take zazza6i Dan Allah kiyi sauri kikaita asibiti ",

Raina ne ya 6aci saboda idan akwai abunda na tsana bai wuce inje asibiti ba , badan komai ba saboda na tsani inbi layin ganin doctor gsky bana juran bin layi duk sai in 'kosa in dawo gida,

A fili kuwa cewa nayi" toh mama ina amina take ?"
Mama tayi mani nuni da cewa tana kan gado kwance,

Zuwa nayi inda amina take kwance na ta6a jikinta sai naji rau kamar wuta saboda zafi cikin sauri na juyo nace ma mama" kai mama jikinta yayi zafi sosai bara naje nacanza kayan jikina sai inzo in kaita asibitin",

Ban jira abunda mama zatace ba nayi saurin juyawa naje ďaki na nacanza kayan jikina zuwa wata doguwar riga abaya, da sauri naje ďakin mama na ďauki amina na goya kasancewar 'karamar yarinya ce,

Mama ta ďauko post ďin ta tabani kuďin napep da wasu kuďin koda za'a tambayi wani abun a asibiti,

Ina zuwa bakin titi ban wani wahala ba nasamu napep nafaďa mashi asibitin da zai kaini,

*AHMAD SANI SPECIAL HOSPITAL* Naje wacce akafi sani da *yariman bakura* wacce take a jihar zamfara gusau ,

Bayan na shiga asibitin sai tunanina ya tsaya cak saboda gaba ďaya narasa inda zan fara zuwa, saboda wannan shine karo na farko dazance nafara zuwa asibiti wai ganin likita,

Ina tsaye ina shawar warin inda zan fara zuwa sai naga wata mata zata wuce ta gaba na, da sauri na isa wajen matar nace" baiwar Allah Dan Allah inada tambaya",

Matar ta juyo ta kalleni tace" Allah yasa nasani ,"
" Dan Allah inda ake ganin Dr nake nema ",

Matar tayi ďan murmushi tace" Ai sai kinje kin fitar da babban file sannan zakiga likita idan kuma sabuwar zuwa ne sai kije kiyanki kati,

Anan tayi mun kwatance inda zanje in fitar da file ďin amina, ni kuma nayi mata godiya na wuce,

Saida nashiga cikin inda ake fitar da file sai naga dubban mutane, abunda na tsana kenan bin layi,

Nan take wata zuciyar ta umurceni da in koma gida ince ance basai tasha kowane magani ba kawai tasha pc wato paracetamol,

Ina nan dai tsaye ina kallon yanayin asibitin saboda wasu gyare gyare da akayi mata kasancewar na daďe banzo ba,

Can nayanke shawarar bara nakoma gida saboda A gaskiya bazan iya jurar bin layin ganin likita ba saboda akwai mutane sosai kasancewar asibitin government ne,

Juyowar da zanyi Idanuwa na sukayi caraf akan wani kyakkyawan mutume mai kyaun sura,

Kai da ganshi kasan cewa wayayyen ďan boko ne kuma maiji da kanshi,

Nan take naji zuciya ta tana bugawa saboda nidai a rayuwa ta ban ta6a sanin miye so ba h asalina bana kula maza dukda cewa akwai masu sona ciki kuwa harda ýan uwa na masu son muyi auren zumunci Amma ko kulasu banayi,

Amma ganin wannan kyakkyawan mutumen yasa naji zuciya ta na bugawa anan take naji nashiga cikin wani yanayi,

'Kura mashi manyan idanu na nayi ina kallon shi yana tahowa inda nake da alama ďakin marassa lafiya zaije,

Anan take naji mutumen yayi masifar burgeni zuciya ta tafara aiyanamun inama ace shine mijina,

Ina nan tsaye mutumen har yazo ya wuce ta gabana ko kallo na baiyi ba, nan take naji raina ya 6aci saboda naga ko kulani baiyi ba,

Kallonshi naci gaba yi harya isa wani ďakin marassa lafiya,
Nan take nayanke shawarar binshi duk inda yaje, saboda na tsinci kaina cikin masifar son wannan mutumen duk da cewa bansan meye so ba Amma tabbas wannan shine so,

Binshi nayi har ďakin danaga ya shiga amma kash securities sun hanani shiga kasancewar ba lokacin visiting bane,

Babu irin ro'kon da banyi masu ba akan subarni in shiga amma suka'ki sai cewa sukayi inbari Dr ya fito sannan inshiga,

Hakan ya 6ata mun rai wai inbari Dr ya fito sannan in shiga basusan wajen shi nazo ba,

Babu yanda zanyi haka nakoma ďayan 6angaren na raku6e ina jiran fitowar shi,

Dr ďin ya daďe sosai a ďakin da alama duba fetions ďin yayi,
Lokacin daya fito ban 6ata lokaci ba nayi saurin zuwa wajen shi,

Kafin in insa haryayi saurin barin gurin dayake cikin ďan sauri sauri yake tafiya,

Ni kuma haka nayi ta binshi cikin raina ina faďin Allah yasa yasa mutumen nan ya soni!

Sauri na'karayi ina binshi shi kuma baimasan inayi ba saboda hankalinshi baya kaina,

Tsayawa naga yayi Ashe wani frand ďinshi ne yagani suna gaisawa, ganin hakan yasa nayi saurin isa wajen su idona a rufe saboda ban ta6a haďuwa da namijin danaji ina masifar so kamar shi ba,

Ina zuwa naje na tari gabanshi na tsaya,
Sai a Lokacin natuna cewa banida abunda zance mashi idan naje wajenshi,

A gabanshi na tsaya duk nabi na ruďe saboda yanda ya kafeni da shanyayyun idanunshi,

Cikin mamaki yace" baiwar Allah lafiya me kike nema ?",
En enna nafara saboda bansan mezance mashi ba,

'Dayan mutumen da suke tsaye ya tsura mun idanu yanason yagane meyake damuna ni kuma saina sunkuyar da kaina 'kasa saboda kunyar da naji ,

Shikam Dr hannu ya sake bawa feand ďinshi yace "abokina saimun hadu wani lokacin", yana gama faďan haka saiya juya yayi tafiyar shi yabarmu tsaye da abokinshi ,

Ni kuma danaga Dr yayi tafiyar shi saina tsaya ina kallonshi shi inajin tsantsar soyayyar shi A raina,

Wannan abokin nashi naji yace mun " Dan Allah baiwar Allah me kike nema ko kinsan shi ne?  "

Murmushin ya'ke nayi nace" Aa wlh ban sanshi ba banma ta6a ganinshi ba yaune farkon haďuwa na dashi ",
Nafaďa ina 'kara kallon inda Dr yabi dan har yayi nisa,

Juyowar da zanyi sai naga mutumen nan shima ni yake kallo ,
Saida mukayi kusan mintuna biyar babu wanda yacema wani komai sai daga baya mutumen yake cemun,

"Nagane manufarki akan Dr dukda cewa bakece mace ta farko da kika fara nuna mashi so ba, bazan 6oye maki ba Dr yanada farin jinin ýan mata",

Du'kar da kaina 'kasa nayi ina wasa da yatsun hannuwa na saboda bazan iya 'karyatashi ba domin gaskiya ya faďa,

Shirun danayi ne yasa yaci gaba da cewa " inason ki bayyanawa dr sageer soyayyar ki ",

Saurin ďago da kaina nayi na kalli mutumen da har yanzu bansan sunanshi ba sai kuma na 'kara du'kar da kaina 'kasa,

Mutumen yace " yes inason ki bayyana mashi soyayyar ki mayb kidace ya amshi tayi soyayyar ki, dan haka yanzu zan baki number shi ",

Bance komai ba mutumen yaci gaba da cewa "karkiji kunya idan kika bayyana soyayyar ki gareshi saboda ba a kanki ne farau ba, karki manta nana KHADIJA matar manzon Allah S.A.W ita tafara nuna soyayyar ta ga annabimu Muhammad S. A.W" ,

Hakan daya faďa mun sai naji sanyi a raina dan haka ban 6ata lokaci ba nakar6i number dr sageer kamar yanda naji yafaďa,

Shima anan yabani tashi number da sunanshi amir a cewar shi idan na dace inkira in faďa mashi,

Haka mukayi sallama inajin daďi cikin raina,

Lokacin dana isa gida cikin ikon Allah jikin Aysha yayi sau'ki sosai dan harda ďan wasan ta takeyi,

Ina zuwa nayima mamanmu bayanin 'karya nace ai dr yayi mata wasu allurai sannan yace basai tasha magani ba amma idan anga jikin yafara zafi to a ji'ka towel da ruwa mai kyau a daddana mata jikin sai kuma a bata paracetamol,

Mamanmu ta yarda da magana ta kuma taji daďi sosai tace aikinga 'kara da akaje asibitin yafi dan ayi maganin ciyon da gaggawa,

Nikam bance mata komai ba nayi saurin shiga ďaki na dan inkira hubby na sunan danasa mashi a waya kenan wato *hubby na*

Ina zuwa na kwanta kan katifa na danna kiran number hubby na.........

*kubiyoni danjin cigaban wannan labarin mai ban tausayi da ban haushi*

*Ummu Meenal ce✍🏻*

*pls share*

No comments:

Post a Comment