*🍡🍡🍡NAFI K'ARFIN SHI🍡🍡🍡*
*NA MRS SADEEQ✍🏻*
*ummu Meenal*
*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
*G.W.F*
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we the best among*
*SADAUKARWA GA MAHAIFINA ALLAH YA QARA MAKA LAFIYA KAYIMUN KOMAI A RAYUWA*
*Comments ďinku yana qaramun qarfin gwiwa dole inyi typing ko banaso, nafi qarfin shi fans nima ina qaunar ku*
*Page 2-5*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*cigaban labari*
Haka ashraf ya koma gidan su ranshi a b'ace saboda wulak'ancin da khady tayi mashi , shi gaba ďaya rayuwar shi bai tab'a samun macen da take yimashi irin abunda khady take mashi ba,
Yana shiga cikin gidan bai tsaya ko ina ba sai ďakin matar yayanshi maman Abdullah dayake a cikin gidan anyi mata nata part ďin saboda mijinta baya zama shine yabarta nan gidan,
Yana shiga falon ya zauna kan kujera ya dafe kanshi ranshi a b'ace,
Maman Abdullah ta tsura mashi ido Dan tasan idan dai taga ranshi a b'ace to bai wuce ace khady ce ta b'ata mashi rai ba,
'Dago fukarshi yayi yace, "matar yaya abunda khady take yimun yayi yawa any a kuwa idan mukayi aure zatayimun biyayya ?,"
"Kayi haquri ashraf me zai hana tayi maka biyayya ko yanzu da kaga tana yimaka haka zata daina idan kunyi aure, "
Cikin rashin k'arfin jiki yace, "Allah yasa Amma gaskiya dole ne nima in San yanda zan gyara mata zama ni abunda yake bani mamaki sai tace tafi k'arfi na bansan me take nufi ba,"
Maman Abdullah taji tausayin ashraf irin son da yakema khady Amma ita bata sonshi, cikin tausaya tace, "kasan khady tanada k'awaye mayb su suke zugata, "
Ashraf yayi saurin girgiza kanshi yace, "tabbas matar yaya hakane Amma yanzu taya zan iya rabata da k'awaye nata?,"
Matar yaya tace, "ni a ganina karkayi mata maganar k'awaye yanzu kabari idan kunyi auren saika hanata tarayya dasu kaga lokacin kanada damar bata comman,"
Baice komai ba ya tashi yabar ďakin ya shiga ďakin shi , kan gadonshi ya kwanta yana tunano rashin kunyar da khady take mashi ,
Zuciyar shi ce take raya mashi ya kira khady Dan yayi mata kashedi da freands ďinta ,
Bai tsaya b'ata lokaci ba ya ďauko wayarshi ya kira khady,
Ita kuma lokacin tana nata ďakin kwance tana tunanin yanda auren ta da ashraf zai kasance,
A zuciyar ta tana tunanin irin wulaqancin da zata yima ashraf idan sunyi aure, wayar ta taji tana ringing daman tana kusa da ita ďauka tayi sai taga ashe ashraf ne ,
Ajiye wayar tayi bata ďauka ba ita kuma wayar taci gaba da ranging, har saida ashraf yayi mata 3miscoll sannan ta ďaga ta yatsine fuska kamar yana kusa da ita,
Sallama yayi mata da qyar ta ansa,
Ashraf shiru yayi saida yaji shirun yayi yawa sannan yace, "khady daman inason zan faďa maki wata magana, "
Shiru tayi batace komai Dan haka ashraf yaci gaba da cewa ,"daman k'awayen kine nasan akwai waďan da basu dace ace kuna tare dasu ba shine nakeson kirabu dasu,"
Dariya sosai khady tayi cikin isa da tak'ama tace, "wallahi baka isa karabani da freands ďina ba kai A matsayinka nawa,?"
"A matsayina na mijinki," yabata ansa A tak'aice,
Dariyar rainin hankali ta'Kara yi sannan tace, "wallahi nafi k'arfin ka nafi qarfin kazama mijina Dan haka karka sake cewa haka tunda ba aure aka ďaura ba,"
Dariyar takaici yayi cikin ranshi yace yarinyar nan saina tashi tsaye da ita , a fili kuwa cewa yayi , "karki manta akwai sadaki na A wajenki kinga kuwa ranar aure kawai muke jira, "
Haushi yabata dayace akwai sadakinshi a wajen ta cikin hasala tace, "to aini bance ka kawo sadakin ka gidanmu ba Dan bana gayyatar ka duka duka sadakin dubu hamsin ne kacal kaga kuwa ni nafi k'arfin dubu hamsin,
"Iyayenki suka yanke maki kuďi da dubu hamsin kinga kuwa sunfiki sanin komai dan haka dubu hamsin shine dai dai ke," yana kaiwa nan ya kashe wayar ya kifa kanshi kan pillow a zuciyar shi yana cewa saina tashi tsaye akan khady Dan Naga raini ya shiga tsakanina da ita,
Ita kuwa khady yana kashe wayar sai taji kamar ya daka mata mashi saboda taji haushin kalaman shi sosai , takaicin ta ďaya dayace dubu hamsin shine dai dai da ita ,
Da sauri ta ďauko wayarta takira wata freands ďinta nana duk ta kwashe yanda sukayi da ashraf ta faďa mata,
Nana tace, "wallahi ashraf so yake ya raina ki tunda har kikaga ya faďa maki haka halan baki faďa mashi cewa ke matar manya bace ke kinfi k'arfin shi,"
Yasan komai nana ďan rainin hankali ne Amma wallahi idan aka aura mun shi saina gasa mashi aha A hannu,"
Nana tace, "aikinki yana kyau kuma ashraf bai isa ya rabamu ba ,"
Anan khady ta kashe wayar tana tunanin yanda zata yima ashraf idan sunyi aure,
*WACECE KHADIJA?*
Khadija Umar shine asalin sunan ta yarinya ce ga alhaji Umar ,khadija fara ce tas tanada kyau na wuce musali kai idan ka kalleta zatayi tunanin aljana ce, komai na Jikin ta kamar ita tayima kanta bakinta ďan qarami,
Haka kuma tanada manyan idanuwan k'wayar idanunta irin na kareena kapoor golden wajen farin kuma fari ne tas kamar madara,
Khady tanada face mai kyau jikinta kuma ďan cib cib batada k'iba haka kuma bazamu kirata ramammiya ba tanada diri hips mazaunai duk lafiyyen namijin da ya kalleta sai hankalin shi ya tashi,
Gashin kanta dogo ne kai gaskiya kyaun ta bai misaltuwa, da wannan k yaun ne k'wayenta suke zugata akan karta auri ashraf wai ita matar manya ce,
Duk da cewa tun tana k'arama yake sonta kuma lokacin itama tana sonshi sai yanzu data girma ne sai tace tafasa aurenshi lokacin freands ďinta Sun zugata ,
Shi kuma babanta dayake magana ďaya ganeshi sai yace bata isa ba ko tana so ko bata so dole sai anyi auren , tunda da farko tace tana sonshi,
Yanzu haka khady tana level 2 inda takeda braind sosai a skull ďin Dan duk makaratar Ana ji da ita kuma kowa so yake ya zama frand ďinta, inda ita kuma A yanzu ganin ashraf take tafi k'arfin shi,
wannan kenan,
*Ummu meenal ce✍🏻*
*yawan comments yawan typing*
No comments:
Post a Comment