*🍡🍡🍡NAFI K'ARFIN SHI🍡🍡🍡*
*NA MRS SADEEQ✍🏻*
*ummu Meenal*
*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
*G.W.F*
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we the best among*
Https://www.facebook.com
*DEDICATED*
*ANTY MAIMUNATH O. G*
*Wannan shafin nakune class of twenty thirteen 💞 nabakushi kyauta kuyi yanda kukaga dama dashi banida bakin magana, 'kaunar ku A gareni tafi 'karfin page, Amma kusani ina sonku sosai,*
*idan nace inkira sunayenku page ďin bazai isa ba saboda kunada yawa Amma duk wacce tasan ita 'yar 2013 ce A G.G.S.S JIBIYA to wannan page nata ne, Ana mugun tare🤝🏻*
*Masoyan Wannan littafi ina godiya sosai Ana mugun tare🤝🏻, Yau read more sai kun gaji🤣*
*page 61-65*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
"Wallahi tsoro nakeji ban iya kwana ďaki ni kaďai ina tsoro, pls kazo mu kwanta ",
Tafaďa kamar zatayi kuka,
Dariya tabawa Ashraf wai tsoro takeji, sabon salo kenan, bata ta6a cewa tanajin tsoro ba sai yau,
'Daure fuskar shi yayi ya kalle ta babu alamun fara'a A tare dashi kamar bai ta6a dariya ba yace
"Ke har zaki iya buďe baki kice baki iya kwana ďaki ke kaďai, karki manta idan nazo korata kikeyi, kuma ni A matsayi na namijin ki ban iya in faďa maki magana kiji ba, kin maida ni wani sakarai dan haka kije kiyi kwanciyar ki babu inda zanje ", ya faďa yana juya mata baya,
Khady sororo tayi tana kallon shi, mamakin shi takeyi yanda ya canza mata lokaci ďaya, wata zuciyar ta tace ke shareshi kawai kije kema kiyi kwanciyar ki,
Haka khady ta juya badan ranta yaso ba taje kan gado tayi kwanciyar ta tareda tunanin Ashraf A zuciyar ta,
Lokacin da Khady ta kwanta tayi zaton barcin zaizo Amma abun mamaki sai juye juye takeyi kan gado ita kaďai, saita ďauko pillow ta rungume sai kuma taji baiyi mata daďi ba sai tayi jifa da pillow,
A b'angaren Ashraf shima haka ya kwana babu daďi saboda ya Saba yana rungeme khady Amma yau gashi ya rungume pillow, haka ya kwana babu daďi da 'kyar yakai safe A haka,
Da safe khady tayi saurin haďama Ashraf breakfast ďinshi saboda yauma taga alamun da wuri zai fita, wanka tayi tasa wata doguwar riga har 'kasa ďinkin yayi kyau sosai,
Lokacin Ashraf harya shirya saboda da wuri zai fita, Amma cikin ranshi yace bazai fita ba saiya jefa khady cikin tunani,
Wayar shi ya ďauko yayi kamar yana kira kuma bai kira kowa ba saiya kara A kunne yayi kamar waya yakeyi harda faďin , Eh sweetheart gani nan zuwa yanzu kijirani,
Gabanta ya faďi da taji Ashraf yana waya tayi saurin dafe 'kirjin ta saboda yanda yake bugawa, cikin ranta ta maimaita sweetheart? ,
Gabanshi ta 'karasa da breakfast ďin, Amma duk da haka bai daina wayar ba saima tashi yayi daga inda ta ajiye breakfast ďin yace mata
" Ai ni banan zanyi breakfast ba Akwai wacce take jirana kuma Idan nace intsaya inyi break to zan 6ata mata lokaci ne ", ya faďa yana tashi tsaye,
Ba'kin ciki fal A zuciyar khady ta kalle shi tace " to koma wacece take jiranka ai yakamata kaci abinci, duba fa abincin jiya ko ta6awa batayi ba ",
Kallon ta yayi yana murmushin mugunta yace " yauma karki girka dani saboda zanci A wajen wadda take sona, dan haka ki girka naki ke kaďai,
Hawaye suka cika mata idanunta harta kasa 6oye su har saida Ashraf yagani, ita kanta tasan cewa Ashraf yana yimata 'kwarjini sosai, tarasa dalilin dayasa idan baici abincin ta ba takejin haushi,
Tarasa dalilin dayasa jiya da basu kwana ďaki ďaya kan gado ďaya ba takasa cikakken barci, ta rasa dalilin dayasa Ashraf yake burge ta A yanzu,
Tana cikin wannan tunanin ne Ashraf yace " matsa sauri nakeyi zan wuce ",
Girgiza mashi kai tayi tana kuka saboda batason ya fita baiyi break ba, kuma koban faďa ba mata Sun sani mace ta tsani tayi girki miji ya'kici ,
Tabawa Ashraf tausayi Amma duk da haka yasa a ranshi saita gane tayi kuskure,
'Daukar ta yayi cak kamar jaririya yaje ya kwantar da ita kan 3siter saboda ta tare mashi hanya,
Yana ajiye ta bai tsaya 6ata lokaci ba ya kama gabanshi,
Ita kam khady kuka ta rin'kayi sosai, tana cikin kukan ne nana takira ta a waya ,
Kallon screen ďin wayar tayi sai taga nana ce dan haka tayi saurin picking tana kuka ,
Nana dataji kukan khady nan take tayi saurin tambayar ta dalilin kukan,
Cikin kuka khady tace " Ashraf Aure zai 'karayi naji yana waya da wata yanzu yana cewa gashinan zuwa ta jirashi , kuma ya daina cin abinci na " ta'karasa maganar tana kuka,
Nana wani irin daďi taji har a zuciyar ta , Amma A fili kuwa cewa tayi " meyasa ya daina cin abincin naki ? ",
" Nidai tun jiya ya canja mun saboda kinsan ya hanani zuwa makaranta shine naje, kuma jiya lokacin da na dawo makaranta na iskeshi a gida tunda daga lokacin ya canja mun ",
Nana tayi ajiyar zuciya tana jin daďi tace " Ashraf bai isa ya hanaki kici gaba da karatun kiba dan haka yanzu ma kitashi kishiya muje makaranta ",
Kwa6e fuska khady tayi ta zaro idanu sai kace tana gaban nana tace " kirufamun asiri yau idan na'kara zuwa ai nashiga uku wajen Ashraf , dan wallahi ya canja mun sosai ",
Nana cikin 6acin rai tace " to tsoron shi kikeji ne ? Yaushe kika fara tsoron Ashraf? Kinga daman inaji maki tsoron Auren Ashraf gashi yanzu har canja maki ",
Khady shiru tayi tana sauraron nana datake ta faďan ta,
Cikin faďan ne nana take cewa ta tashi taje makaranta saboda kartayi massing lectures ďinta,
Khady tace " nana gaskiya bazanje ba saboda inajin tsoron abunda zai biyo baya , Amma Kibari zan lallashi Ashraf ďin yabarni in 'karasa karatu na ",
Haushi ya hana nana magana wai zata lallashi Ashraf yabarta taci gaba da karatu, wani irin kishi ya mamaye nana dan haka batayi magana ba tayi saurin kashe waya,
Ita kam khady nana tana kashe waya taji kanta yana ciyo daman ga rashin barcin jiya dan haka taje kan gado tayi kwanciyar ta,
Ashraf yana fita daga gida sai yaji khady tabashi tausayi Amma bai nuna hakan ba saboda yanason yayima hankali dan yaga da sauranta har yanzu,
Tunda Khady ta kwanta tana barci bata tashi ba sai wajen qarfe biyun rana,
Da sauri ta tashi tashiga toilet tayi alwala tayi sallah harta shiga kitching da niyyar tayi girki sai maganar Ashraf ta faďo mata a zuciya inda yake cewa , karta ďora girki dashi kotayi ma baci zaiyi ba,
Nan take taji ranta ya 6aci, tayi dana sanin abunda tayi mashi, tanason tayi mashi girki Amma bata son Ashraf ya'ki ci,
Wata dabara ta faďo mata a rai, wayar ta tayi saurin ďaukowa ta kira Ashraf, yaune karo na farkon kiran number Ashraf,
Ashraf yana ganin wayar Shi tana ringing yana dubawa yaga khady ce, mamaki sosai yayi saboda bata ta6a kiranshi ba, idanma takirashi to ba kiran arzi'ki bane,
Saida wayar tayi ringing har sau biyu bai ďauka ba Ana uku ne ya ďauka tareda sallama,
Khady tanajin muryan Ashraf sai taji gabanta ya faďi tarasa dalilin yin hakan kodan bata saba bane ,
Cikin in inna khady tace " ya office? " sosai Ashraf yaji daďin kulawar Khady Amma saiya danne yace " Alhamdulillah ",
"Daman nakira ne inji me kakeso in Girka maka ? " ta 'karasa maganar kamar wacce batada gaskiya,
A 6angaren Ashraf kuwa cewa yayi " nop kibarshi aina faďa maki kokinyi girkin bazan ciba, ",
Shiru tayi tarasa mezatace mashi tana son tabashi ha'kuri Amma tanajin girman kai,
Shi kam Ashraf dayaji shirun yayi yawa saiya kashe wayar yaci gaba da harkokinshi,
Khady ta zauna jugum ta dafe kanta tana tunanin wai shin meyake faruwa da ita ne ,
Fita daga kitching ďin tayi saboda yin girkin bashida amfani tunda Ashraf bazaici ba ,
Haka khady ta wuni sai taji duk babu daďi saboda Ashraf ďinta yana fushi da ita, abunda yake 'kara ďaga mata hankali shine wacece wannan wadda Ashraf yake waya da ita ? Taji yana kiranta da sweetheart shin wane matsayi take A burinshi ? Kodai Auren ta zaiyi ?,
Batada mai ansa mata tambayoyin ta, Amma tasama ranta koma wacece saita raba tsakaninsu, wata zuciyar Tata tace khady kodai son Ashraf kikeyi ? ,
A fili ta furta Nooo *NAFI 'KARFIN SHI* ,
Tunda Ashraf ya fita bashine ya dawo ba sai dare, Lokacin khady tana falo abun mamaki wai tana jiran Ashraf ya dawo, karo na farko kenan tun auren su,
Yana dawowa khady ta mik'e tsaye tana faďin sannu "Sannu da zuwa , " tana kar6ar jakar hannunshi ,
" yauwa "
"Ya aiki ? "Alhamdulillah , ya school ďin naki ?" yafaďa yana shigewa bedroom,
Kallonshi khady takeyi kamar tace bataje makaranta ba sai taga ya shige bedroom yabarta nan tsaye, hakan yabata haushi sosai,
Tunani tayi kotaje tabawa Ashraf ha'kuri, hakan tayi ta shiga bedroom da niyyar tabashi ha'kurin laifinta na jiya,
Tunani yazo mata na cewa kotaje tabashi ha'kuri laifin da tayi jiya,
Bata tsaya 6ata lokaci ba ta shiga bedroom ďin taga yana cire kayan jikin shi ,
Tsayawa tayi a 'kofar sai taga ya yimata 'kwarjini sosai, jin tayi kamar taje ta tayashi cire kayan Amma bataga fuskar yin hakan ba ,
A hankali take takawa har taje gabanshi inda suke facing ďin juna ta tsaya,
Ashraf ya tsura mata idanu a ranshi yanajin kamar ya rungume ta saboda yayi missing ďin ta, Amma idan yayi hakan ya 6ata wasan shi dan haka ya 'kara ďaure fuska yace
" lafiya kikazo nan kikayi tsaye ? "
Anan khady ta daburce ta rasa mezatace mashi Dan gaba ďaya batayi tunanin abunda zatace mashi ba idan tazo ,
Shikam dayaga batada niyyar yimashi magana saiya ďauko jallabiyar shi yasa ya fice daga gidan ,
Dafe kanta tayi tana tunanin daman haka Ashraf yake da zuciya ? Tana cikin wannan tunanin sai taji wayar Ashraf tana ringing, Ashe ya manta bai fita da wayar ba,
Da kamar karta ďauka sai taji tanason tasan wanda ya kira wayar ,
Zuwa tayi inda wayar take ringing ta duba sai taga kamar tasan number,
Picking call ďin tayi Amma da akaji muryan ta sai akayi saurin kashewa,
Abun yabawa khady mamaki saita ta6e baki tace koma Waye shiyasani,
'Daukar wayar tayi tashiga gurin massage (khady da karambani ) inbox tashiga anan taga abunda ya ďaga mata hankali , massage ďin love tagani a wayar Ashraf kuma sai tana ganin kamar tasan number,
Karanta massage ďin tafarayi duk na love ne nan take taji kishi ya rufe ta , wani massage tagani wanda yafiyi mata ciyo inda akace yaje gida yanzu yagani khady ta fita zuwa makaranta,
Nan take tafara tunanin wane munafikin ne wannan ,
Wayar ta taďauko tasa wannan number da akeyima Ashraf massage tasa a nata wayar,
Mamaki da firgici suka bayyana a fuskar khady inda taga sunan nana 'karara akan wayar ta,
Tana cikin mamaki saiga Ashraf yadawo, saurin kallonshi tayi, tayi editing number nana tace " wannan number da ake turo maka massages ta Waye ? "
" Number nana ce , "
Cikin tsananin mamaki khady tace " wace ala'ka ce tsakanin ka da nana ? "
" budurwa ta ce kuma ita nakeson in aura nan bada daďewa ba ",............
*Ummu meenal ce ✍🏻*
No comments:
Post a Comment